Tsohon mataimakin kwamishinan ’yan sanda da aka dakatar, Abba Kyari, ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa gidaje sama da 20 da Hukumar NDLEA ta ce mallakinsa ne, na mahaifinsa ne da ya rasu, kuma suna karkashin rabon gado tsakanin ’ya’yan gidan kusan 30. Kyari ya fara kare kansa ne a gaban Mai Shari’a James Omotosho, inda ya ce wasu daga cikin kadarorin ma an riga an sayar da su domin biyan kudin maganin mahaifinsa kafin ya rasu.

Ya ce ba zai iya saka wadannan kadarorin cikin takardar bayyana dukiyarsa ba saboda har yanzu ba a raba gado ba, don haka ba shi da kaso na musamman da zai iya ikirarin mallaka. Ya kara da cewa abin da ke cikin dokar bayyana dukiya shi ne a saka kadarorin da mutum yake da cikakken mallaka karara.

Kyari dai na fuskantar tuhuma 23 daga NDLEA kan boye kadarori, canza sunan mallaka, da kuma sarrafa kudaden da ake zargi cewa sun saba ka’idojin doka. Hukumar ta ce tana da shaidu da takardu na bankuna da ke nuna mu’amalolin kudi da aka danganta da shi, yayin da Kyari ya ce kudaden da ake magana akai yawancin su kudaden aikin tsaro ne da aka rika tura masa don gudanar da manyan ayyuka.

Alkalin ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba domin ci gaba da gurfanar da shaidu, tare da jaddada cewa kotu ba ta yanke hukunci kan ko Kyari na da laifi ba tukuna, har sai an kammala sauraron bayanan bangarorin biyu.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version