Wata gobara da ta tashi da safiyar Litinin 02 ga Fabrairu ta ƙone wasu shaguna a kasuwar Singa dake a birnin Kano. Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta fara ne tun da sassafe, inda ta lalata wasu shaguna.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 3:16 na asuba. Ya ce nan take jami’an kashe gobara suka isa wajen domin shawo kan wutar da hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan kasuwar.
Ya ƙara da cewa har zuwa kusan ƙarfe 10 na safe, akwai wasu wurare da har lokacin wutar ke ci, yayin da jami’ansu ke aiki tukuru domin shawo kan lamarin gaba ɗaya. Hukumar ta ce za ta fitar da ƙarin bayani ga manema labarai bayan an kammala aikin kashe gobarar.
