Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda biyu da babban sakatare, domin ƙarfafa gudanar da ayyukan gwamnati a fannoni daban-daban na jihar. An gudanar da bikin rantsuwar ne a yau Juma’a a fadar Gwamnatin Kano, yayin zaman majalisar zartarwa karo na 32.
Daga cikin waɗanda aka rantsar akwai Barrister Abdulkarim Kabir Maude SAN, wanda ya zama sabon Babban Lauyan Jihar Kano kuma Kwamishinan Ma’aikatar Shari’a. Haka kuma, an rantsar da Dr. Aliyu Isa Aliyu a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Bunƙasa Harkokin Kiwo, sabuwar ma’aikata da gwamnati ta kirkira domin inganta fannin kiwon dabbobi a jihar.
Bugu da ƙari, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kuma rantsar da Barrister Salisu Muhammad Tahir a matsayin Babban Sakatare na Ma’aikatar Shari’a. A yayin bikin rantsuwar, gwamnan ya shawarci sabbin jami’an gwamnati da su kasance masu gaskiya, rikon amana da kuma jajircewa wajen gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da bin doka da oda a dukkan matakai.
Gwamnan ya ce nadin sabbin kwamishinonin ya samo asali ne daga cancanta, gogewa da irin gudummawar da suka bayar ga al’ummar Kano. Ya taya su murna tare da bayyana fata cewa za su taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin gwamnati da bunkasa ci gaban jihar.
