Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika takardun daukar aiki na dindindin ga sababbin malaman Lissafi 400 da aka tura manyan makarantun sakandare a fadin jihar. Wannan mataki dai na zuwa ne domin cike gibi a fannin koyar da lissafi, wanda ake ganin yana jawo raguwar nasara a jarrabawa da kuma tasirin karatun dalibai a fannoni daban-daban.

A cewar shugaban ma’aikatar yada labaran gwamnati, Sunusi Bature Dawakin Tofa, Gwamna Yusuf ya ce lissafi shi ne ginshikin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, don haka dole ne a gina karfi tun daga matakin sakandare domin Kano ta samu damar gogayya a duniyar ilimi mai dogaro da fasaha.

Gwamnan ya bayyana cewa shigar wadannan malaman zai inganta yadda ake koyarwa, ya kara wa dalibai kwarewa, tare da karfafa hanyoyin da za su bi domin shiga fannin STEM (Science, Technology, Engineering and Mathematics). Ya kuma yaba wa Ma’aikatar Ilimi da hukumar KSSSSMB bisa yin zaben malaman cikin gaskiya da tsari.

Ya gargadi sababbin malaman da su koyar da himma, kishin aiki da kwarewa, domin su tabbatar sun yi wa jihar rikon amana. Ya ce gwamnati na da kwarin gwiwar cewa daukarsu zai samar da babban tasiri ga makarantun sakandaren Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version