Jam’iyyar APC ta sanar da cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zai karɓi katin zama mamba na jam’iyyar ta hanyar tsarin rijistar lantarki a ranar Talata, 20 ga Janairu, 2026.
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayyana hakan a yayin wani taron jam’iyya, inda ya ce shirin na daga cikin sabon tsarin rijistar mambobi da ake aiwatarwa a fadin ƙasar nan.
A cewarsa, manufar shirin ita ce ƙara gaskiya da inganci a tsarin jam’iyyar, tare da bin sahun wasu jihohi da suka fara rijistar domin ƙarfafa APC da tafiyar da siyasar zamani a Nijeriya.
