Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da komawa All Progressives Congress (APC). Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Nuhu Anka, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Sanarwar ta ce gwamnan ya yanke wannan shawara ne bayan tuntuba da shugabannin siyasa, dattawa da magoya baya a jihar. An ce matsalolin cikin gida da rikice-rikicen shugabanci da ke addabar PDP a matakin ƙasa da na jiha na daga cikin dalilan da suka sa ya sauya sheƙa.

Haka kuma an bayyana cewa gwamnan ya ce zai ci gaba da mayar da hankali kan inganta tsaro da ci gaban Zamfara, yana mai cewa shiga APC zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya domin amfanin al’ummar jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version