Gwamnatin Jihar Kano ta karyata jita-jitar da ke yawo cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin tsige Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Gwamnatin ta ce babu wani shiri ko niyya na sauya Sarkin bayan sauya sheƙar gwamnan daga NNPP zuwa APC.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da Aminiya a ranar Juma’a, 31 ga Janairu 2026. Ya ce an naɗa Sarki Sanusi II ne bisa doka bayan soke tsohuwar dokar masarautu, kuma hakan ba zai sauya ba.
Sanusi Bature ya jaddada cewa Sarki Sanusi II har yanzu shi ne halastaccen Sarkin Kano. Ya ce babu wani yunƙuri ko ƙarin gyaran da gwamnati ke shiryawa da zai shafi matsayin sarkin a halin yanzu.


