Gwamnan Jihar Kano ya kai ziyara ta musamman domin jajanta wa Malam Haruna, mutumin da aka kashe masa iyali mutum bakwai a unguwar Dorayi, inda ya bayyana alhini da juyayin wannan mummunan lamari da ya girgiza al’umma.

 

A yayin ziyarar, gwamnan ya ba Malam Haruna kujerar aikin Hajji da Umara, tare da yin alkawarin sayo masa sabon gida domin ya bar gidan da lamarin ya faru. Haka kuma, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Kano za ta dauki nauyin yi masa aure da zarar komai ya dai daita, kuma gwamnatin za ta dauki nauyin kula da shi da sabuwar matar tasa gaba ɗaya.

 

Bugu da ƙari, gwamnan ya ce dan uwan Malam Haruna mai suna Umar, wanda ke taimaka masa wajen ɗebe kewa, zai rika tafiya tare da shi duk inda zai je, inda gwamnati za ta dauki nauyin dukkan tafiye-tafiyen da za su yi tare, a matsayin tallafi da goyon baya gare su.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version