Gwamnatin Jihar Kwara ta bayyana cewa ta biya bashin fansho da ya kai naira biliyan 3.3 da ta gada daga tsohuwar gwamnati, domin rage tarin bashin da ake bin tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi a fadin jihar. Kamar yadda Kwamishiniyar Kudi, Dr. Hauwa Nuhu, ta bayyana a Ilorin yayin taron manema labarai na zango na uku na shekara ta 2025, gwamnatin ta ce ta gaji bashi da ya kai naira biliyan 19 tun daga shekarar 2009, inda har yanzu naira biliyan 12 daga ciki aka iya biya.

A cewar Nuhu, an kammala biyan hakkokin ma’aikatan kananan hukumomi har zuwa shekarar 2011, yayin da aka ware naira biliyan 2.5 domin biyan bashin shekarun 2012, 2013 da 2014. Ta kuma ce biyan fansho na ma’aikatan jiha ya kai har zuwa shekarar 2016, duk da cewa har yanzu ana bin gwamnatin naira biliyan 22. Don rage wannan nauyi, gwamnatin ta ware naira biliyan 5.6 daga kudaden harajin cikin gida na zangon uku na 2025 domin ci gaba da biyan waɗannan hakkoki.

Kwamishinar ta bayyana cewa jihar ta samu naira biliyan 15.7 daga harajin cikin gida a zango na uku na shekarar 2025, kuma duka an tura su kai tsaye zuwa asusun gwamnati na Treasury Single Account (TSA) domin tabbatar da gaskiya da bin doka. Ta ce jimillar bashin cikin gida na jihar yanzu ya kai naira biliyan 57, wanda ya haɗa da fansho da bashin ma’aikata.

Dr. Nuhu ta danganta yawaitar bashin fansho da aiwatar da karin albashi na ₦30,000 da ₦70,000 da gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq ta kaddamar. Sai dai ta tabbatar da cewa gwamnati na ci gaba da biyan bashin a hankali tare da bayyana komai a fili ga jama’a. “Babu wani abu da muke ɓoyewa — kowane ɗan Kwara na iya ganin yadda ake aiwatar da kasafin kudin mu a shafin gwamnati,” a cewar ta.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version