Gwamnatin jihar Neja ta sanar da gaggawar rufe dukkan makarantun jihar bayan da ’yan bindiga suka sace ɗaliban makarantar St. Mary mai zaman kanta da ke garin Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara. Lamarin, wanda ya faru cikin mako, ya sake tayar da hankalin jama’a a tsakiya Najeriya.

Gwamna Umaru Bago ne ya bayyana matakin yayin ganawa da manema labarai a Minna, inda ya ce gwamnatin jiha ba za ta yi wasa da rayukan ɗalibai ba, musamman ganin yadda hare-haren yan bindiga ke ƙara kamari a yankin. Ya ce rufe makarantun ya zama dole don kare sauran ɗalibai daga barazanar tsaro.

A cewar Gwamna Bago, gwamnatin Neja ta kuduri aniyar ceto ɗaliban cikin koshin lafiya, lamarin da ya ce ya girgiza al’umma matuƙa. Wannan mataki, in ji shi, na cikin dabarun da hukumomin tsaro ke aiki da su domin tabbatar da zaman lafiya.

Gwamnan ya bayyana harin a matsayin abin takaici da bakin ciki, yana mai jaddada cewa gwamnatin jiha ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an dawo da ɗaliban da kuma tabbatar da cewa makarantun jihar sun koma aiki cikin kwanciyar hankali nan gaba kadan.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version