Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, ya bayyana cewa matsalar tsaro ce babbar damuwarsa a halin yanzu, musamman a Arewacin ƙasar. Ya ce dole ne a ɗauki matakan gaggawa domin dawo da zaman lafiya, gina amana da haɗin kai tsakanin al’umma. Tinubu, wanda Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya wakilta, ya yi wannan jawabi ne a bikin cika shekaru 25 da kafuwar Arewa Consultative Forum (ACF) tare da kaddamar da Asusun tallafawa ayyukanta.

A cewar shugaban, gwamnati ta gada matsalolin tsaro masu rikitarwa, amma tana kokarin magance su da gaggawa da zuciya ɗaya. Ya ce ba za a samu cigaban tattalin arziki da ilimi ba muddin ta’addanci da fashi da makami ba su ƙare ba. Tinubu ya kuma nuna kyakkyawar fatan cewa Arewacin Najeriya zai koma matsayinsa na ƙarfi, yana mai ambaton yiwuwar fitar da man fetur daga gonakin mai na Kolmani da sauran yankuna. Shugaban ya ce dole Arewa ta faɗi gaskiya ba tare da jin tsoro ba domin kare al’umma masu rauni.

Ya kuma bayyana muhimmancin manyan ayyukan gine-ginen da ake ƙoƙarin kammalawa, ciki har da titin Abuja–Kaduna–Kano, yana mai nanata cewa shugabannin yankin za su ci amanar al’umma idan suka yi shiru yayin da talakawa ke fama da yunwa da tsoro. Tinubu ya yabawa ACF bisa rawar da ta taka na tsawon shekaru 25 wajen kare mutunci, gaskiya da adalci ga al’ummar Arewa, yana mai cewa wannan jubili na musamman tamkar bikin ƙarfin hali da jajircewa ne.

Shugaban ya bukaci shugabanni daga kowane mataki su sake sabunta alkawarin bin akidu masu kyau da suka kafa ACF, domin dorewar zaman lafiya da cigaban Arewa wanda shi ne ginshiƙin zaman lafiyar Najeriya gaba ɗaya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version