A ranar Lahadi, 23 ga Nuwamba 2025, wani Farfesa na fannin Magungunan Ciki da Koda a Jami’ar Niger Delta da ke Bayelsa, Oghenekaro Egbi, ya bayyana cewa cutar chronic kidney disease (CKD) a matsayin wadda take kan gaba wajen zama sanadin mutuwa ta biyar a duniya, inda ya tabbatar da cewa akalla ’yan Najeriya 230,000 na bukatar dashen koda ko jinyar dialysis domin tsira.
A cewarsa, hawan jini, ciwon suga, kiba, da cututtukan kamuwa da kwayoyin cuta kamar hepatitis da HIV ne suka dagula al’amura, tare da haifar da nauyin cututtuka biyu a lokaci guda. Ya ce sama da kashi 68% na marasa lafiya da ake kwantarwa a wani babban asibiti a Bayelsa na fama da cututtukan da ba a yaduwa, tare da kara da cewa halin rayuwa da cin abinci na zamani — musamman abincin da aka sarrafa sosai — shi ma yana haddasa mummunar illa ga koda.
Ya kara da cewa bincikensa ya nuna cewa shan lemo, kayan gwangwani, nama da aka sarrafa, noodles, da sauran kayan da ke dauke da sinadarai masu yawa na kara hadarin cutar da kashi 24%. A nan ne ya ce muhalli ma na da tasiri, inda ya bayyana cewa mutanen Obunagha — yankin da ake harkan kona iskar gas — sun fi fama da matsalolin koda fiye da mazauna Azikoro da ba a samun gas flare. Bechi Hausa ta gano cewa talauci da tsadar jinya na kara jefa marasa lafiya cikin halin kaka-ni-ka-yi, inda mafi yawan masu dialysis ba sa iya ci gaba da jinya har mako guda.
Farfesan ya ce a kasashen da suka ci gaba kusan kashi 30% na masu cutar koda mataki na ƙarshe ana musu dashen koda, amma a Najeriya kasa da mutum 1 cikin 100 ne ke samun wannan damar saboda rashin kudade, karancin kayan aiki da kuma ƙarancin sani. Don haka ya bukaci gwamnati ta inganta manufofi, fadakar da jama’a, da kara zuba jari a bangaren kiwon lafiya domin rage wannan barazana mai karuwa ga al’umma.
