A ranar Lahadi, 23 ga Nuwamba 2025, Ƙungiyar Ƙwadago ta Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (NUEE) ta yi kakkausar barazanar dakatar da duk wasu ayyukan samar da wutar lantarki a faɗin Najeriya. Wannan na zuwa ne bayan harin da ta ce wasu jami’an ’yan sanda masu ɗauke da makamai suka kai wa ma’aikatanta a tashar Egbu 132/33kV Transmission Substation da ke Owerri, Jihar Imo.

Ƙungiyar ta bayyana cewa harin ya haifar da firgici da tashin hankali ga ma’aikatan da ke wurin, lamarin da ta ce ya saɓa wa ka’idojin aiki da kare haƙƙin ma’aikata. NUEE ta ce jami’anta suna gudanar da ayyukansu na yau da kullum ne aka afka musu da duka da barazana, abin da ta bayyana a matsayin cin zarafi da gaza kiyaye mutuncin ma’aikaci.

A cewar sanarwar da sakataren ƙungiyar ya fitar, NUEE ta gargaɗi gwamnati da shugabannin rundunar ’yan sanda cewa za ta rufe dukkan tashoshin wutar lantarki muddin ba a ɗauki matakin hukunta masu laifin ba tare da tabbatar da tsaron mambobinta ba. Bechi Hausa ta tattaro cewa ƙungiyar ta jaddada cewa ba za ta lamunci irin wannan take haƙƙin ma’aikata ba.

Ƙungiyar ta nanata cewa ta gaji da kallon yadda jami’anta ke fuskantar barazana yayin da suke gudanar da ayyukan raya ƙasa. Ta ce lokaci ya yi da gwamnati za ta tabbatar da tsaron ma’aikatan wutar lantarki domin kauce wa tsayawar wuta a dukkan sassan ƙasar idan ba a ɗauki gaggawar mataki ba.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version