Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da gagarumin sauyi a tsarin shirin bautar ƙasa na NYSC, inda za a maye gurbin shugabancin sojoji da na farar hula, tare da tsawaita zaman atisaye a sansani daga makonni uku zuwa shida. An amince da sauye-sauyen ne a taron majalisar na ranar Litinin da aka gudanar a Abuja.
Ministan Matasa, Ayodele Olawande, ya ce sauye-sauyen za su mayar da NYSC cibiyar da ke haɓaka ƙwarewa da samar da aiki. Ya ce za a yi amfani da fasaha wajen kiran masu yi wa ƙasa hidima, a tura su bisa la’akari da tsaro, sannan a ba su horo kan shugabanci, kasuwanci, ƙwarewar zamani da sana’o’in da suka dace da karatunsu.
Haka kuma, za a raba masu yi wa ƙasa hidima zuwa fannoni 11 bisa iliminsu da burinsu na aiki, yayin da za a sake fasalin shirin atisaye na makonni shida zuwa matakai uku. Gwamnatin tarayya ta ce an fara shirin wannan garambawul tun shekarar 2025, domin ƙarfafa rawar da NYSC ke takawa wajen bunƙasa matasa da tattalin arzikin Najeriya.
