Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa, akwai wani sabon yunƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi, na hana jam’iyyar ADC shiga zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, 29 ga Yuni, 2026.

Atiku ya ce ya samu sahihan bayanai, da ke nuna ana ƙoƙarin amfani da hanyoyin siyasa da shari’a, domin hana ADC shiga zaɓen, yana mai cewa, jam’iyyar na samun karɓuwa a tsakanin ’yan Najeriya. Ya kuma yi kira ga al’umma, su kare dimokuraɗiyya, tare da ƙin amincewa da duk wani yunƙurin tauye haƙƙin zaɓe.

Ya kuma buƙaci ɓangaren shari’a ya kasance mai zaman kansa, tare da kira ga INEC, hukumomin tsaro, ƙungiyoyin farar hula da ƙasashen duniya su sanya ido kan shirye-shiryen zaɓen 2027.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version