Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta karyata ikirarin Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya sake sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ake kira “Countries of Particular Concern” (CPC) saboda zargin cin zarafin ’yancin addini. Trump ya yi wannan ikirari ne inda ya bayyana cewa ana kashe Kiristoci da dama a Najeriya ta hannun ‘yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayi, yana mai cewa Kiristanci na fuskantar barazana a kasar.
Sai dai a martanin da ta fitar a yau Asabar ta hannun kakakinta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya ta ce wannan zargi bai dace da gaskiyar halin da ake ciki a kasar ba. Ta bayyana cewa ’yan Najeriya na zaune lafiya ba tare da bambancin addini ba, kuma gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da yaki da ta’addanci da inganta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.
Gwamnatin ta ce tana godiya ga damuwar Amurka kan kare hakkin dan Adam da ’yancin addini, amma ta jaddada cewa Najeriya kasa ce mai bin doka da ka’ida wadda ke kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ba tare da nuna bambanci ba.
Ta kara da cewa Najeriya za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka domin karfafa fahimtar juna da kuma tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Afrika ta Yamma da ma duniya baki daya.
