Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa wani malami mai shekaru 19 da haihuwa, Abdullahi Abbass, hukuncin daurin rai da rai bayan ta same shi da laifin yi wa dalibinsa mai shekaru tara fyade. Hukuncin ya biyo bayan bincike da shari’a da hukumar NAPTIP ta gudanar kan lamarin da ya faru a makarantar da ke yankin Kwali a ranar 19 ga Maris, 2025.
Rahoton ya bayyana cewa Abbass, wanda shi ne malamin ajin su yaron, ya tura wani ɗalibi ya kira wanda aka ci zarafi daga gidansu bayan makaranta, sannan ya ja shi zuwa wani wuri kusa da gidansa inda ya aikata mummunan laifin fyade da shi ta hanyar da ta sabawa dabi’a. Bayan faruwar lamarin, yaron ya sanar da mahaifiyarsa, wadda ta kai rahoto ga hukumomi, kuma hakan ya kai ga kama da gurfanar da malamin.
Kotun da Mai Shari’a M. Osho–Adebiyi ke jagoranta ta same shi da laifi a bisa tanadin dokar Violence Against Persons (Prohibition) Act, 2015, wadda ke tanadar hukuncin daurin rai da rai ga masu aikata irin wannan mummunan laifi. Shugabar NAPTIP, Hajiya Binta Adamu Bello, ta bayyana jin daɗinta da hukuncin, tana mai cewa hakan zai zama izina ga sauran masu niyyar aikata laifukan fyade da cin zarafi a ƙasar.
Ta kuma gode wa ‘yan sanda bisa haɗin kai da saurin gudanar da bincike, tare da tabbatar da cewa sunan Abbass zai shiga cikin rajistar masu laifin fyade a Najeriya. Wannan hukunci ya zo ne bayan wani irin shari’a makamancinsa a Anambra, inda wani malami, Pascal Ofomata, ya samu hukuncin shekaru 12 a gidan yari kan cin zarafin ɗalibinsa a 2025.
