Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta shigar da ƙara a gaban kotu kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin katsalandan da satar bayanan wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
A cewar takardun kotu da aka shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, gwamnatin ta zargi El-Rufai da amsa cewa shi da wasu mutane sun shiga bayanan sadarwar wayar Ribadu ba bisa ka’ida ba, lokacin da yake hira a wani shirin talabijin a ranar 13 ga Fabrairu, 2026. Ana zargin hakan ya saɓa dokar hana aikata laifukan yanar gizo da kuma dokar sadarwa ta Najeriya.
Takardun ƙarar sun kuma ce El-Rufai ya amince yana da alaƙa da mutanen da suka aikata wannan katsalandan amma bai kai rahoto ga hukumomin tsaro ba, abin da ake ganin laifi ne a ƙarƙashin dokar kasa. Haka kuma ana zarginsa da amfani da na’urori ko tsarin fasaha domin shiga bayanan sadarwar, lamarin da gwamnati ta ce ya barazana ga tsaron ƙasa.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a bayyana ranar da za a gurfanar da El-Rufai a gaban kotu ba, yayin da ake sa ran shari’ar za ta ja hankalin jama’a sosai duba da muhimmancin mutanen da lamarin ya shafa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version