Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya ta gargadi al’ummar Najeriya cewa za a iya samun ruwan sama mai yawa da zai haifar da ambaliyar ruwa a wurare 39 da ke cikin jihohi 16 daga ranar 4 zuwa 8 ga Oktoba, 2025. Wannan gargadi ya fito ne ta cikin danarwar da Cibiyar Farko ta Gargadin Ambaliyar Ruwa ta Ƙasa, kuma Daraktan Sashen Kula da Kogin Ruwa da Ƙasa, wadda Usman Bokani ya sanyawa hannu a kai.
Jihohin da abin zai shafa sun haɗa da Delta (Asaba), Yobe (Damaturu), Sokoto (Isa), Zamfara (Anka, Bungudu, Gusau, Kaura-Namoda, Maradun, Shinkafi), Katsina (Jibia), Oyo (Kisi, Oyo), Kebbi (Ribah, Sakaba, Yelwa), Kano (Gwarzo, Sumaila, Karaye), da kuma Niger (Kontagora, Mashegu, Mokwa, New-Bussa, Rijau, Wushishi). Sauran sun haɗa da Kwara (Kosubosu), Benue (Agaku, Buruku, Gboko, Katsina-Ala, Ugba), Borno (Briyel), Bayelsa (Brass, Ikpidiama, Odoni), Cross River (Edor, Ikom), Rivers (Itu, Ahoada), da Enugu (Nsukka).
Ma’aikatar ta shawarci gwamnatocin jihohi da hukumomin da abin ya shafa da su ɗauki matakan gaggawa domin rage illolin ambaliyar da ake sa ran faruwa. Ta kuma bukaci jama’a su kasance cikin shiri da bin shawarwarin hukumomin ceto don kare rayuka da dukiyoyi.
Rahotannin Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun nuna cewa daga farkon Satumba zuwa 20 ga wata, akalla mutane 232 ne suka mutu, yayin da sama da 121,000 suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta shafi sassa daban-daban na ƙasar. Jimillar mutane 339,658 ne ambaliya ta shafa a bana, inda 681 suka ji rauni iri daban-daban.
