Gwamnatin Tarayya ta amince da sake buɗe iyakar Tsamiya da ke jihar Kebbi zuwa Jamhuriyar Benin domin bunƙasa kasuwancin ketare. Hukumar Kwastam ta ƙasa ta tabbatar da cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya ba da amincewar.

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba da matakin, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta haɗa kai da Hukumar Kwastam da sauran jami’an tsaro domin tabbatar da cewa buɗe iyakar ba zai janyo barazana ga tsaron ƙasa ba. Ya kuma jaddada shirye-shiryen tallafa wa iyalan jami’an kwastam da aka kashe a yankin tare da ba da motocin Hilux guda biyu don taimaka wa ayyukan tsaro.

Shugaban Hukumar Kwastam na ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya ce za a buɗe iyakar ne bisa ƙa’idojin tsaro masu tsauri don hana masu laifi cin gajiyar hanyoyin kasuwanci. Ya bayyana cewa za a yi amfani da tsarin ICT domin haɗa bayanan kwastam na Najeriya da na Benin da Nijar, tare da gargadin cewa duk wata mota da aka samu ta kauce hanya za a ƙwace ta.

Shugaban Ƙungiyar Manoman Albasa ta Ƙasa, Isa Aliyu, ya ce buɗe iyakar Tsamiya na da matuƙar muhimmanci ga manoma da ’yan kasuwa, ganin yadda albasa ke lalacewa da wuri. Ya ƙara da cewa matakin zai ƙara GDP, samar da ayyukan yi, da inganta tattara haraji, tare da rage safarar haramtattun kaya ta hanyoyin ɓoye.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version