Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar da shirin dakatar da ɗaukar nauyin tallafin wutar lantarki ita kaɗai, inda za a yi hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi daga shekarar 2026. Daraktan Babban Ofishin Kasafi na Ƙasa, Dr. Tanimu Yakubu, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin wani taron horaswa ga ma’aikatu kan shirye-shiryen kasafin kuɗin 2026.

Ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin a fito da gaskiya kan kuɗaɗen tallafin wutar lantarki, a riƙa bibiyarsu tare da raba su bisa adalci tsakanin matakan gwamnati. A cewarsa, ɓoye irin waɗannan kuɗaɗe na haifar da bashin da ba a gani da rikice-rikice a kasuwar lantarki, inda ya jaddada cewa duk wani sauƙin farashi yana haifar da gibi da dole a biya.

Yakubu ya ƙara da cewa sabon tsarin ba hukunci ba ne, illa dai daidaita alhakin kowa don ƙarfafa inganci a fannin lantarki. Ya bukaci ma’aikatu su bayyana kuɗaɗen tallafi a kasafin 2026, tare da guje wa tura nauyin bashin da ba a tanada masa kuɗi ba zuwa kasuwar wutar lantarki.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version