Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta ja da baya kan sauye-sauyen tattalin arziki da ta fara ba, duk da radadin da aka fuskanta a farko. Ya ce sauye-sauyen sun zama wajibi domin ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya da samar da damammaki ga matasa.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Talata yayin da yake karɓar tawagar Bankin Duniya ƙarƙashin jagorancin Daraktar Ayyuka, Anna Bjerde, a Fadar Aso Rock. Ya jaddada muhimmancin sauya fasalin noma ta hanyar injina, tallafa wa manoma, inganta shirin tsirrai da kuma amfani da takin zamani na cikin gida.
Shugaban ya kuma ce matakan cire tallafin man fetur da haɗa farashin canjin kuɗi sun kasance masu wahala amma dole, yana mai cewa duk da tashin farashi da aka samu da farko, yanzu darajar naira ta daidaita. A nata ɓangaren, Bjerde ta yaba da jajircewar Tinubu kan sauye-sauyen, tana mai cewa sakamakon da Najeriya ta samu cikin shekaru biyu abin yaba ne a idon duniya.
