Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da cewa harin sama na haɗin gwiwa tsakanin sojojin Najeriya da Amurka ya kai hari kan wuraren ’yan ta’adda a Ƙaramar Hukumar Tangaza, tare da cewa babu fararen hula da suka rasa rayuka a yayin aikin.

A cikin sanarwar da Darakta Janar na Yaɗa Labarai, Abubakar Bawa, ya fitar, gwamnatin ta ce har yanzu ana ci gaba da tantance sakamakon harin, don haka ba a kammala fahimtar cikakken tasirin aikin ba a wannan lokaci.

Gwamnatin ta kuma ce an fara bincike kan wasu abubuwa da aka gano kusa da garin Jabo a Ƙaramar Hukumar Tambuwal, tana mai jaddada goyon bayanta ga haɗin gwiwar tsaro da ƙasashen waje, tare da kira ga jama’a da su ba jami’an tsaro haɗin kai domin dawo da zaman lafiya a jihar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version