Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa matsalar ’yan bindiga da sauran kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya za su zo ƙarshe daga shekarar 2026, yana mai kira ga ’yan ƙasa da su haɗa kai domin samun ƙasa mai zaman lafiya.
Akpabio ya yi wannan jawabi ne yayin taron addu’a da azumi da aka shirya domin girmama iyalinsa a Cocin Methodist Cathedral of Unity da ke Ukana Ikot Ntuen, Jihar Akwa Ibom, inda ya jaddada cewa cigaban ƙasa ba zai samu ba sai an samu zaman lafiya da haɗin kai.
Ya kuma bukaci ’yan Najeriya, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, da su goyi bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a yaƙin da ake yi da ’yan bindiga da ta’addanci, yana mai cewa haɗin gwiwa da ƙasashen waje da kuma haɗin kan iyalai na da muhimmanci wajen cimma nasarar kawo ƙarshen rashin tsaro.
