Majalisar Dokoki ta bayar da umarnin sake wallafa (re-gazetting) manyan dokokin gyaran haraji guda huɗu, bayan ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan zargin cewa an yi wasu sauye-sauye bayan an amince da su. Wannan umarni ya fito ne a ranar Jumma’a, 26 ga Disamba, 2025. Inda majalisar ta jaddada cewa matakin na da nufin kare sahihancin kundin dokoki ne kawai, ba wai amincewa da wani kuskure ba.

A cikin wata sanarwa da kakakin Majalisar Wakilai, Akin Rotimi, ya fitar, ya ce shugabannin majalisun biyu sun umurci Sakataran Majalisar Ƙasa da ya sake wallafa dokokin tare da fitar da Certified True Copies (CTCs) na dokokin da aka amince da su yadda ya kamata. Dokokin sun haɗa da Nigeria Tax Act, 2025, Nigeria Tax Administration Act, 2025, Joint Revenue Board of Nigeria Act, 2025, da kuma Nigeria Revenue Service Act, 2025, bayan jama’a sun fara nuna damuwa kan yadda aka daidaita su, aka tura su ga shugaban ƙasa, da kuma yadda aka wallafa su a Mujallar Gwamnati.

Rotimi ya bayyana cewa majalisar ta kafa kwamitin wucin-gadi na mutum bakwai domin bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa ana tafiyar da komai ne cikin ikon doka da tsarin majalisa, ba tare da shisshigi daga waje ba. A cewar majalisar, wannan mataki ba zai shafi haƙƙoƙi ko ayyukan sauran sassan gwamnati ba, kuma za a ci gaba da sanar da jama’a yayin da binciken ke tafiya. Majalisar ta kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su kwantar da hankalinsu, su bar hukumomin majalisa su kammala aikinsu cikin gaskiya da bin doka.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version