Hukumar Kwastam ta Nijeriya (NCS) ta yi gargaɗi ga masu neman aiki a hukumar a zangon daukar ma’aikata na 2025 da su yi watsi da wasu sakonninbda su ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin nuna jerin sunayen wadanda aka zaɓa daga kowace jiha domin tantancewa. Hukumar ta bayyana irin wannan bayanin a matsayin ƙarya kuma ba shi da tushe. A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin X a ranar Asabar mai taken “Unverified Social Media Post on 2025 Nigeria Customs Service Recruitment Exercise,” hukumar ta ce sakon bai fito daga gare ta ba ko daga kowane kafar sadarwa na hukuma.

Hukumar ta jaddada cewa tsarin tantancewa zai kasance cikin gaskiya da adalci, bisa cancanta, kuma cikin ka’idojin da suka dace da na duniya. Ta kuma tunatar da jama’a cewa duk wani muhimmin bayani game da daukar ma’aikata ana sanar da shi ne kai tsaye ga wadanda suka shiga jerin masu cin gajiyar tsarin, ta hanyar shafi na musamman na sabunta bayanai: https://updates.customs.gov.ng. Hukumar ta bayyana cewa daukar ma’aikatan da ta fara a ranar 27 ga Disamba, 2024 ya jawo aikace-aikace 573,523 daga rukunan Superintendent, Inspectorate da Customs Assistant. Daga cikin su, mutum 286,697 ne suka tsallake matakin tantance takardu kuma aka gayyace su zuwa jarrabawar kwamfuta (CBT) ta farko, wadda aka gudanar a matakai domin tabbatar da adalci da inganci.

Bayan kammala wannan matakin na farko, an bayyana cewa dukkan rukunin sun shiga CBT, amma wadanda suka yi nasara a rukunin Superintendent kadai aka gayyata zuwa mataki na biyu. Wannan mataki ya gudana ne a cibiyoyi da aka ware a shiyyoyi shida na ƙasar kamar yadda aka sanar tun farko. Hukumar ta kuma jaddada cewa tana bin tsarin “Federal Character” domin tabbatar da daidaito a daukar ma’aikata daga dukkan yankuna.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version