Hukumar Zaɓen Najeriya Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa ba za ta amince da Kabiru Tanimu Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar PDP ba, sakamakon shari’o’in da har yanzu ke gaban kotu. Hukumar ta ce wannan matsaya ta ta’allaka ne da tanade-tanaden doka da kuma hukuncen kotuna da ke da alaƙa da batun shugabancin jam’iyyar.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 22 ga Disamba, wadda sakataren INEC, Dakta Rose Oriaran-Anthony, ta sanyawa hannu, kuma jaridar Punch ta ruwaito. A cewar INEC, ta ɗauki matakin ne bayan karɓar wasiƙu daga lauyoyin PDP da ke buƙatar a gyara bayanan shugabannin jam’iyyar na ƙasa a rumbun bayanan hukumar, bisa zaɓen da aka yi a babban taron jam’iyyar a jihar Oyo a watan Nuwamba.
Sai dai INEC ta ce bayan duba da nazari mai zurfi kan buƙatun da aka gabatar—tare da la’akari da gaskiyar lamari, dokoki da kuma hukuncen kotuna—ta kai ga matsayar cewa ba za ta sa ido ko amincewa da sakamakon taron da aka gudanar a ranar 15 ga Nuwamba, 2025 ba, har sai an kammala shari’o’in da ke gaban kotu.
