Wasu jami’an rundunar tsaro ta NSCDC sun tsere domin tsira da rayukansu bayan wani mummunan hari da wasu ƴan bindiga suka kai wa ofishin rundunar a ƙauyen Ibrahim Leleh, da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa ƴan bindigar, masu yawa, sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 4:00 na asubahin ranar Talata, inda suka buɗe wuta kan jami’an tsaron da suka tarar. Harin ya tilasta wa jami’an NSCDC shiga cikin daji domin gujewa rasa rayuka.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun ƙwace ikon ƙauyen tare da kwashe makaman jami’an rundunar. Kakakin NSCDC a jihar Neja, Abubakar Rabi’u, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce rundunar na tattara bayanai domin ɗaukar matakan da suka dace.
