Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin ƙarshe na kwace manyan filaye biyu da aka tanada domin gina Goodluck Jonathan Legacy Model Housing Estate, bayan ta ayyana su a matsayin kadarorin da ake zargin sun samo asali ne daga haramtacciyar hanya. Mai shari’a Mohammed Umar ne ya yanke hukuncin a safiyar Laraba, 24 ga Disamba, 2025, bayan Hukumar ICPC ta shigar da ƙara, yayin da lauyan kariya bai nuna adawa ba.
Kotun ta bayyana cewa filayen, da ke Kaba District a Abuja, suna da faɗin murabba’in mita sama da 279,000, kuma an kiyasta darajarsu da kusan Naira biliyan 5.28. Mai shari’a Umar ya umarci ICPC da ta sa ido kan kammala gina gidaje 962 da aka tsara a wurin, tare da haɗin gwiwar Bankin Lamuni na Gidaje na Ƙasa (FMBN), domin tabbatar da cewa gidajen sun kai ga masu ƙaramin ƙarfi kamar yadda aka tsara tun farko.
Binciken ICPC ya nuna cewa an fitar da duk kuɗin aikin—kimanin dala miliyan 65—ga kamfanin da aka ba kwangilar, duk da cewa ba a gina ko gida ɗaya ba. Haka kuma an bayyana cewa akwai yunkurin sayar da filayen ga jama’a, lamarin da kotu ta ce zai iya lalata ƙoƙarin dawo da kadarorin gwamnati. Saboda haka, kotun ta umurci a mika filayen ga FMBN tare da kafa kwamitin haɗin gwiwa domin ganin an aiwatar da aikin yadda ya dace kuma ya amfani al’umma.
