Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bukaci Kwamishinan ’Yansandan Jihar Kano da ya gaggauta janye jami’an tsaron da ke gadin Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan Sarkin Nasarawa. Kwankwaso ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025, yayin jawabi a bikin kaddamar da rundunar tsaro mallakin gwamnatin Jihar Kano da aka gudanar a birnin Kano.

A cewarsa, Muhammadu Sanusi na II ne kaɗai halastaccen Sarkin Kano, yana mai jaddada cewa duk wani yunƙuri na kafa wani sabon tsarin sarauta a jihar ba zai taimaka wajen samar da zaman lafiya ba. Ya ce ba za a iya tilasta nada sarki ta hanyar amfani da jami’an tsaro ba, yana mai gargadin cewa hakan na iya ƙara ruruta rikici da tayar da hankalin al’umma.

Kwankwaso ya kuma soki matakin ajiye Aminu Ado Bayero a gidan Sarkin Nasarawa, yana cewa hakan bai dace da al’adun Kano da martabar masarautar ba. Ya bukaci hukumomin tsaro da su yi aiki bisa tanadin doka da umarnin gwamnati, domin kauce wa duk wani abu da ka iya janyo tashin hankali, musamman a wannan lokaci da ake ci gaba da takaddamar shari’a kan masarautar Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version