Ƙungiyar Haƙar Ma’adanai ta China a Najeriya ta musanta rahotannin da ke zargin cewa kamfanonin China na kutsawa harkar ma’adanai ta ƙasar nan tare da aikata ayyukan ba bisa ƙa’ida ba. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 23 ga Disamba, 2025, tana mai cewa rahoton da aka wallafa a ranar 11 ga Disamba mai taken “Conquest: The Chinese Infiltration of Nigeria’s Solid Minerals Sector” ya ƙunshi bayanai marasa inganci da suka ruɗar da jama’a.

A cewar ƙungiyar, dukkan kamfanonin haƙar ma’adanai na China da ke aiki a Najeriya suna bin dokoki da ƙa’idojin ƙasar nan, tare da haɗin gwiwa da hukumomin gwamnati domin inganta tafiyar da harkar. Ta ce kamfanonin sun zuba jari a cibiyoyin sarrafa ma’adanai a cikin gida, sun ɗauki ‘yan Najeriya aiki, lamarin da ya ƙara samar da ayyukan yi da kuma ƙara darajar abin da ƙasar ke samu daga albarkatun ma’adanta.

Ƙungiyar ta kuma yi watsi da zargin cewa kamfanonin China na da alaƙa da ayyukan ta’addanci, tana mai cewa wannan zargi ba shi da tushe. Ta jaddada cewa su ma kamfanonin sun sha fama da matsalar rashin tsaro, kuma suna shirye su ci gaba da haɗa kai da gwamnatin Najeriya wajen kare tsaro, kare muhalli, da tallafa wa al’ummomin da ke kewaye da wuraren haƙar ma’adanai, domin ƙarfafa dangantakar China da Najeriya da kuma bunƙasa tattalin arzikin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version