Iran ta tabbatar da mutuwar Jagoran Addininta, Ali Khamenei, bayan hare-haren haɗin gwiwar United States da Israel suka kai a ranar Asabar. Kafafen yaɗa labaran gwamnati sun ce jagoran mai shekaru 86 ya rasu tare da ’yarsa da surukinsa da jikansa, suna bayyana rasuwarsa a matsayin shahada.
Gwamnatin ta sanar da kwanaki 40 na zaman makoki na ƙasa baki ɗaya, tare da jaddada cewa Khamenei ya sadaukar da rayuwarsa domin kare Iran. Ya jagoranci ƙasar tun 1989 bayan rasuwar wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci, Ruhollah Khomeini, kuma ya kasance mai iko kan manyan sassan gwamnati da rundunonin tsaro.
Rasuwarsa na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka ta yi tsami tsakanin Iran da kasashen yamma, musamman Amurka da Isra’ila. Tuni shugabannin ƙasashen suka taba yin kalaman barazana a baya, lamarin da ke ƙara ɗaga hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.


