Wani jami’i a Iran ya shaida wa kamfanin dillancin labaran ƙasar, Islamic Republic News Agency (IRNA), cewa mutum 40 ne suka mutu sakamakon harin da ake zargin Israel ta kai wata makarantar firamare ta ’yanmata a garin Minab, lardin Hormozgan da ke kudancin ƙasar.
Gwamnan lardin, Mohammad Radmehr, ya ce fiye da mutum 48 sun jikkata, yana mai gargadin cewa adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa. Lamarin ya janyo kaɗuwa da fargaba a yankin, yayin da ake ci gaba da tantance girman ɓarnar.
Sai dai kafar yaɗa labarai ta BBC ta ce har yanzu ba ta tabbatar da sahihancin rahoton ba, kasancewar ana hana manyan kafofin watsa labarai na duniya shiga Iran, lamarin da ke taƙaita damar samun bayanai masu zaman kansu.


