Shugabannin jam’iyyar NNPP na mazaɓar Gargari a Karamar Hukumar Dawakin Tofa sun sanar da dakatar da Shugaban Jam’iyyar na jihar Kano, Dr. Hashimu Sulaiman Dungurawa. Shugaban mazaɓar, Shu’aibu Hassan, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai.
A cewarsu, an dakatar da Dungurawan ne saboda zargin tada fitina da korar muhimman ’yan jam’iyya ba bisa ƙa’ida ba. Sun kuma ce ya aikata zagi da aibata Gwamnan Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, lamarin da suka ce ya saba wa ƙa’idojin jam’iyyar.
Haka zalika, an zarge shi da ƙin halartar tarukan masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar da yi mata zagon ƙasa. Jam’iyyar ta ce matakin ya zama wajibi domin kare mutunci da martabarta, musamman a wannan lokaci da take fama da rikicin cikin gida kan batun sauya sheƙar gwamnan zuwa APC.
