Jam’iyyar NDC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja, wadda ta soke umarnin da ya tilasta wa INEC yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa. Jam’iyyar ta ce ba a soke rajistarta ba, kuma dukkan harkokinta za su ci gaba kamar yadda aka tsara.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, mambobin NDC a Majalisar Wakilai da ƙungiyoyin Obidient da Kwankwasiyya, sun soki hukuncin kotun. Sun ce matakin na iya tauye dimokuraɗiyya tare da raunana jam’iyyun adawa gabanin zaɓen shekarar 2027.

Shugaban NDC na ƙasa, Moses Cleopas, ya ce lauyoyin jam’iyyar sun fara shirye-shiryen ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, yana mai jaddada cewa babu wani umarni da ya soke rajistar jam’iyyar. Jam’iyyar ta zargi wasu da ƙoƙarin takaita sararin dimokuraɗiyya ta hanyar amfani da kotuna domin dakile jam’iyyun adawa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version