Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bayar da beli ga tsohon ministan shari’ar Najeriya, Abubakar Malami, tare da wasu daga cikin iyalinsa. Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yanke hukuncin bayar da belin a kan kudi naira miliyan 200 ga kowane daga cikinsu tare da mutane biyu da za su tsaya musu.
Kotun ta gindaya sharadin cewa dole daya daga cikin masu tsaya musu ya mallaki gida a unguwar Maitama ko Asokoro, wadanda ke daga cikin manyan unguwannin birnin. Haka kuma kotun ta umurci wadanda ake tuhuma su mika fasfo dinsu ga kotu yayin da za su ci gaba da zama a gidan yari har sai sun cika sharuddan belin.
Kotun ta sanya ranar 16 ga Maris domin fara sauraron shari’ar, inda ake zargin Malami da iyalinsa da hannu wajen karkatar da kudade kimanin naira biliyan 8.7 ta hanyar wasu kamfanoni da kuma sayen kadarori.


