Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafin da wani ɓangare na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya shigar, inda ya nemi a soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta Abuja ta yanke a ranar 31 ga Oktoba. Hukuncin dai ya hana Independent National Electoral Commission (INEC) amincewa da babban taron ƙasar jam’iyyar da aka yi a Ibadan, Jihar Oyo, ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, wanda aka zaɓi Turaki a matsayin shugaban jam’iyyar.
Tun da farko babbar kotun tarayya ta rushe shugabancin Turaki, tana mai cewa an shirya taron da aka zaɓe shi ba bisa ƙa’ida ba. Daga nan ne ɓangaren Turaki ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.
Sai dai a zamanta na yau, kotun ɗaukaka ƙarar ƙarƙashin jagorancin alƙalai uku ta yanke cewa ƙorafin PDP ba shi da tushe, tare da tabbatar da cewa babbar kotun tarayya ta yi daidai. Har ila yau, kotun ta ci tarar naira miliyan biyu ga ɓangaren Turaki kan shigar da ƙarar ba bisa ƙa’ida ba.


