Wata babbar kotun tarayya da ke birnin Abuja ta umarci Independent National Electoral Commission (INEC) da ta yi rajistar sabuwar jam’iyya mai suna National Democratic Party (NDP), bayan kotun ta tabbatar cewa kungiyar ta cika dukkan sharuddan da doka ta tanada.
Mai shari’a Mohammed Umar, wanda ya yanke hukuncin a ranar 16 ga Fabrairu, 2026, ya ce masu neman rajistar sun bi dukkan ka’idojin kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokar zabe ta 2022. Kotun ta kuma soke wata wasiƙa da INEC ta aike a watan Disambar 2025 wadda ta nuna kin amincewa da rajistar, tana mai bayyana ta a matsayin marar inganci.
Haka kuma, kotun ta ba INEC umarnin gaggauta yin rajistar jam’iyyar tare da ba ta dukkan hakkoki da damarmakin da kowace jam’iyya mai rajista ke da su, ciki har da ba ta takardar shaidar rajista. Kotun ta ce idan har ba a yi rajistar ba, to a dokance za a ɗauki jam’iyyar a matsayin wadda aka riga aka yi wa rajista bisa tanadin dokar zabe.


