Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga hannun Independent Corrupt Practices Commission (ICPC) jim kaɗan bayan Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta sake shi daga tsarewa, inda ake zarginsa da aikata laifuka masu nasaba da satar bayanan sirri. Rahotanni sun ce EFCC ta sake shi ne a daren Laraba, amma nan take jami’an ICPC suka karɓe shi domin ci gaba da bincike.
An bayyana cewa El-Rufai ya je hedikwatar EFCC da ke Abuja tun ranar Litinin domin amsa tambayoyi, inda ya kwashe kwanaki uku a tsare. Ana tuhumarsa ne da zargin sa hannunsa a sauraron wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ba bisa ƙa’ida ba, zargin da gwamnatin tarayya ta kai gaban kotu.
Rahotannin da Kakaki24 ke samu sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara a gaban Federal High Court, inda ake tuhumar tsohon gwamnan da laifuka uku ƙarƙashin dokar hana laifukan yanar gizo da kuma dokar sadarwa. Haka kuma, jami’an tsaro sun ƙwace fasfo dinsa domin hana shi fita ƙasashen waje yayin da ake ci gaba da bincike.
Bugu da ƙari, hukumar tsaron farin kaya DSS ta sake buɗe bincike kan ɓacewar wani malami, Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata, tun shekarar 2019. Rahotanni sun ce ana kuma duba wasu saƙonnin kafafen sada zumunta da ‘ya’yan El-Rufai suka wallafa, yayin da hukumomi ke ci gaba da zurfafa bincike kan lamarin.


