Ƙungiyar likitoci ta Nigerian Association of Resident Doctors, ta fara yajin aiki a yau Talata 7 ga Afrilu, 2026, lamarin da ke barazana ga ayyukan asibitocin gwamnati a faɗin ƙasar. Rahoton ya nuna cewa likitocin sun shafe jimillar kwanaki 51 suna yajin aiki tun bayan hawan mulkin Bola Tinubu.
Yajin aikin na yanzu ya samo asali ne daga dakatar da aiwatar da sabon tsarin alawus na ƙwararru da gwamnati ta yi, wanda aka cimma yarjejeniya a kai bayan yajin aikin 2025. Ƙungiyar ta bayyana matakin a matsayin abin takaici, tana mai cewa gwamnati ce ta tilasta musu sake shiga yajin aiki.
Likitocin na buƙatar a dawo da tsarin alawus ɗin, a biya bashin albashi da karin girma, da kuma biyan alawus na watanni 19 da ake binsu. Sun kuma nemi a saki kuɗin horar da likitoci na shekarar 2026, yayin da suka ce za su iya dakatar da yajin aikin idan gwamnati ta janye matakin da ta ɗauka.
