Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana damuwarsa kan yadda matasan Najeriya ke ƙara nuna ɓacin rai game da halin da kasar ra shiga na matsin tattalin arziki. Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi 12 ga Oktoba, inda ya ce ya gana da wata kungiya ta matasa daga jihohin Arewa 19 waɗanda suka koka kan zaben magudi da matsin tattalin arziki da ke shafar rayuwarsu ta yau da kullum.

Atiku ya ce matasan sun bayyana masa cewa suna jin cewa kuri’unsu ba sa tasiri a zabe, yayin da manufofi da rashin ingantaccen mulki ke lalata kasuwanci da rayuwar jama’a. Ya ce, “Kullum idan na zauna da matasa suna korafi kan rashin kyakkyawan shugabanci, magudin zaben da kuma matsin rayuwa, sai na ji matuƙar takaici.” Ya ƙara da cewa kwanan nan ya karɓi tawagar matasa daga jihohin Arewa 19 ƙarƙashin jagorancin Alhaji Adamu Bappa Gombe, inda suka jaddada irin wannan damuwa.

A martaninsa, Atiku ya shawarci matasan da kada su yanke ƙauna, yana mai jaddada cewa canji ba zai samu ba sai ta hanyar akwatin zaɓe. Ya ce ya ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da shiga harkar siyasa da zaɓe domin su zama ɓangare na samar da shugabanci na gari. Ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan ƙarancin yawan masu kaɗa ƙuri’a, yana mai cewa kaso 25 zuwa 30 cikin 100 na halartar zaɓe a kowanne zagaye ba abin alfahari ba ne.

Atiku, wanda ya kasance Mataimakin Shugaban Ƙasa daga 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin mulkin Olusegun Obasanjo, ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da yakar masu adawa da tsarin dimokuraɗiyya. A halin yanzu, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) tare da tsohon abokin hamayyarsa Peter Obi, a wani yunƙuri na kafa ƙawancen adawa domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version