Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai tashi zuwa Italiya a yau Lahadi 12 ga Oktoba domin halartar taron shugabannin ƙasashe kan tsaro da ake kira Aqaba Process Heads of State and Government Level Meeting. Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa taron, wanda za a fara ranar 14 ga Oktoba, zai mayar da hankali ne kan matsalolin tsaro da ke addabar yankin Afirka ta Yamma.

Taron Aqaba wanda Sarkin Jordan, Abdullah II, ya ƙaddamar a 2015, na gudana ne ƙarƙashin jagorancin masarautar Jordan tare da haɗin gwiwar gwamnatin Italiya. An tsara shi domin samar da tsari na haɗin gwiwa wajen yaƙar ta’addanci da sauran barazanar tsaro. Shugabanni da manyan jami’an tsaro daga sassa daban-daban na Afirka za su halarci taron domin tattauna hanyoyin magance ƙalubalen da ke ƙara ta’azzara a yankin.

Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu zai yi amfani da taron wajen ganawa da wasu shugabannin ƙasashe domin lalubo sabbin dabaru da haɗin gwiwa wajen magance matsalar tsaro. A cikin tawagarsa akwai Ministan Tsaro, Badaru Abubakar; Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Ojukwu; Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu; da Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA), Mohammed Mohammed.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version