Wani rikici mai tayar da hankali ya barke tsakanin sojoji da jami’an ‘yan sanda a Bauchi, wanda ya kai ga rasuwar wani ɗan sanda mai suna Constable Ukasha Muhammed. Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Ahmed Wakil, ya fitar ranar Asabar 11 ga Oktoba. An ce arangamar ta faru ne a yankin Bayan Gari na cikin garin Bauchi a ranar 10 ga Oktoba, 2025.

Bisa ga bayanan rundunar, lamarin ya samo asali ne lokacin da tawagar sintiri ƙarƙashin jagorancin Inspector Hussaini Samaila ta isa gaban Otel Padimo, inda wasu biyu suka kai hari ga Constable Ukasha. Ƙungiyar ta yi gaggawar kama ɗaya daga cikin mutanen, wanda daga baya aka gano shi da Private Usman Mubarak, soja mai aiki da Rundunar Hadin Gwiwa a Jos. Wannan kama ta fusata wasu sojoji biyu da suka dawo wajen, dauke da bindigogi kuma cikin kayan soja.

Wakil ya bayyana cewa sojojin biyu — Private Yakubu Yahuza da Private Godspower Gabriel — sun nufi tawagar ‘yan sandan kai tsaye suka bude wuta kan Constable Ukasha, suka harbe shi a kirji sannan suka tsere daga wajen. An garzaya da jami’in zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Rundunar ‘yan sanda ta Bauchi ta tabbatar da kama sojojin da ke hannu tare da kaddamar da cikakken binciken. Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya kafa ƙungiyar kwararrun masu binciken kisa domin tabbatar da adalci. Haka kuma, ya yi kira ga jami’ai da su kwantar da hankalinsu yayin da bincike ke gudana, tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, yana addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version