Dangote Refinery ta sanar da rage farashin man fetur daga naira 1,175 zuwa naira 1,075 kan kowace lita, wanda ke nuna ragin naira 100. Sanarwar da matatar ta wallafa a shafinta na X ta ce an dauki matakin ne sakamakon saukar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma sabon tsarin farashi da kamfanin ya fitar.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizal daga naira 1,620 zuwa naira 1,430 kan kowace lita. Kamfanin ya ce matakin na daga cikin kokarinsa na daidaita farashi tare da saukaka wa masu amfani da makamashi a kasar.

Matatar ta jaddada kudurinta na taimakawa wajen karfafa tsaron makamashi a Najeriya tare da la’akari da halin tattalin arzikin da ‘yan kasa ke ciki. Wannan ne karo na farko da aka rage farashin bayan karin sau uku a jere da aka yi a makonnin baya wanda ya sa farashin man ya yi matukar tashi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version