Ɗan Rabiu Musa Kwankwaso, kuma Kwamishinan Matasa da Wasanni na Jihar Kano, Mustapha Rabiu Kwankwaso, ya ajiye muƙaminsa a gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Matakin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnan ke komawa jam’iyyar APC, lamarin da ke nuna wani sabon babi a siyasar jihar Kano.

A wani saƙo da ya fitar, Mustapha Rabiu Kwankwaso ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa damar da ya ba shi na hidimta wa al’ummar Kano, yana mai cewa ya samu darussa masu yawa a lokacin da ya yi a matsayin kwamishina, tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa ga jihar Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version