Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce mutum 80 daga cikin masu ibada da aka sace sun koma gidajensu lafiya, makonni bayan aukuwar lamarin. Mutanen na daga cikin mutum 177 da aka yi garkuwa da su daga coci uku a Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru.
Kakakin rundunar, DSP Mansur Hassan, ya shaida cewa mutanen sun tsere ne a ranar da aka sace su, lokacin da ’yan bindigar ke ƙoƙarin kwashe su zuwa wani wuri. Ya ce bayan tserewar, sun ɓuya a wasu ƙauyuka na kusa tsawon makonni kafin su koma gida.
DSP Mansur ya ce an tantance mutanen tare da duba lafiyarsu, sannan aka haɗa su da iyalansu. Ya ƙara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutum 87 da har yanzu ke hannun masu garkuwa da mutane.
