Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta karɓi wasu ’yan Najeriya 131 da suka makale a birnin Agadez na Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin shirin dawowar masu son komawa gida na hukumar ƙasa da ƙasa ta ƙaura (IOM), tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya.

A cewar sanarwar da NEMA ta fitar a shafin X, waɗannan mutanen sun iso filin jirgin sama na Aminu Kano da safiyar Alhamis, 30 ga Oktoba, 2025 da ƙarfe 5:17 na safe. An ce jami’an NEMA tare da na Hukumar ’Yan Gudun Hijira (NCFRMI), Hukumar Shige da Fice (NIS) da wasu hukumomi sun tarbe su, inda aka gudanar da rijista da tantance su don tabbatar da sahihancin bayanansu.

An bayyana cewa daga cikin waɗanda suka dawo akwai maza 118, mata hudu, yara maza biyu da yara mata bakwai. NEMA ta ƙara da cewa an samar musu da abinci, ruwa, kula da lafiya, motar asibiti da taimakon sufuri domin tabbatar da dawowarsu cikin mutunci da aminci.

Wannan aikin na cikin shirin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da dawowar ’yan ƙasa cikin girmamawa da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin NEMA, IOM, da sauran abokan hulɗa don karfafa tsarin taimakon ɗan adam da inganta ka’idar ƙaura cikin tsari. A makon da ya gabata ma, NEMA ta tabbatar da dawowar wasu ’yan Najeriya 153 daga ƙasar Chadi.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version