Jam’iyyar NNPP ta yi watsi da ƙudirin da wasu ’yan majalisar dokokin Amurka suka gabatar na sanya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso cikin jerin masu takunkumi.

’Yan majalisar sun nemi a hana shi biza tare da ƙwace kadarorinsa bisa zargin take ’yancin addini.

Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP na Ƙasa, Ladipo Johnson, ya ce Kwankwaso bai aikata wani laifi ba da zai sa a zarge shi da tsattsauran ra’ayi.

Ya buƙaci a yi cikakken bincike kafin yanke hukunci, yana tambayar dalilin ware shi kaɗai kan batun dokar Shari’a a Kano.

Jam’iyyar ta ce Kwankwaso ya taɓa yaƙi da Boko Haram tare da kyautata alaƙa da shugabannin Kiristoci a lokacin da yake gwamna.

Ta kuma nuna cewa ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023 tare da Kirista a matsayin mataimaki, abin da ta ce ya nuna kishinsa ga haɗin kan ƙasa.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version