Ƙungiyar Nigerian Economic Summit Group (NESG) ta bayyana cewa Najeriya na iya cin gajiyar rikicin da ke tsakanin Amurka/Isra’ila da Iran, inda ƙasar za ta iya samun karin kuɗaɗen shiga daga man fetur da ya kai tsakanin Naira tiriliyan 2.3 idan rikicin bai daɗe ba zuwa Naira tiriliyan 30 idan rikicin ya daɗe.

A cikin wata takardar manufofi da ƙungiyar ta fitar a ranar Juma’a, ta ce wannan damar za ta dogara ne da yadda gwamnatin Najeriya za ta mayar da martani ga rikicin. NESG ta ce tashin farashin mai a duniya na iya ƙara kuɗin shiga da kuɗaɗen musayar waje, amma kuma hakan na iya haifar da hauhawar farashi a cikin gida saboda tsadar makamashi da sufuri.

Ƙungiyar ta kuma gargaɗi cewa matsalolin da ke cikin ɓangaren man fetur, hauhawar farashi da kuma matsin lambar kashe kuɗaɗe a lokacin siyasa na iya rage ribar da ƙasar za ta samu. Ta ba gwamnati shawarar ta adana kuɗin da za a samu, ta ƙarfafa tsare-tsaren kuɗi, tare da tallafa wa marasa ƙarfi ta hanyoyin da aka tsara domin kare tattalin arzikin ƙasar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version