Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta faɗa cikin rikici yayin da shugabannin jihohinta suka rabu kan taron ƙasa da za a gudanar a Abuja. Taron dai za a yi ne karkashin ɓangaren da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, amma wasu shugabanni sun ce bai kamata a gudanar da shi ba saboda shari’ar da ke gaban Kotun Ƙoli.

Shugaban PDP na Edo kuma shugaban ƙungiyar shugabannin jihohi, Tony Aziegbemi, ya ce taron ba bisa ƙa’ida ba ne, yana mai gargadin ‘yan jam’iyya da su kaurace masa. Haka kuma reshen jam’iyyar a Sokoto ya sanar da cewa ba zai halarta ba, yayin da wasu jihohi kamar Kwara da Kebbi suka tabbatar da za su halarta tare da tura wakilansu.

Ana sa ran wakilai kusan 2,500 za su halarci taron da za a gudanar a filin Moshood Abiola National Stadium, inda ake shirin tabbatar da sabbin shugabanni. Sai dai rikicin ya ƙara tsananta bayan wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar sun nesanta kansu daga taron, yayin da Wike ya ce za a ci gaba da sulhu duk da sabanin da ke cikin jam’iyyar.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version